Shawara

Nassi yana ƙarfafa neman shawara mai hikima da bin ta, yana nanata rawar da take takawa wajen samun nasara, hikima da shiriya. Akasin haka, ƙin shawarar masu ibada ko bin shawarar mugaye yana kawo kasawa, faɗa, har ma da hallaka.

Ana ƙarfafa neman shawara

...bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora, (Karin Magana 1:5)
...da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba, (Karin Magana 1:25)
...da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata, (Karin Magana 1:30)
Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara. (Karin Magana 12:15)
Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara. (Karin Magana 13:10)
Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima. (Karin Magana 19:20)
Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa. (Karin Magana 20:18)
Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki. (Karin Magana 27:9)
Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara. (Mai Hadishi 4:13)
A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.” (Luka 13:31)

Ana ƙarfafa samun masu ba da shawara da yawa

Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara. (Karin Magana 11:14)
Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara. (Karin Magana 15:22)
Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi; don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa. (Karin Magana 24:5-6)

Ƙarin mutane yana ƙara yawan aiki

Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku. (Firistoci 26:8)
Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi! In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai? Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa. (Mai Hadishi 4:9-12)

Misalan ba da shawara da bin ta

Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?” Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah. Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.” Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne. Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba. Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.” Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa. (Fitowa 18:14-24)
Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba? Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon. (1 Sarakuna 1:11-12)
“Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata. Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su. Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara. (Ayuba 29:21-23)

Misalin rashin ba da shawara ko rashin bin ta

Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa. Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?” Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.” (2 Tarihi 25:14-16)

Inda ake samun shawara

Ubangiji

“Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne. (Ayuba 12:13)
Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini. (Zabura 16:7)
To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa. (Zabura 25:12)
Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai. (Zabura 32:8)
Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane. Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. (Zabura 33:10-11)
Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. (Zabura 73:24)
Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika. (Karin Magana 19:21)
Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. (Ishaya 9:6)
Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji, (Ishaya 11:2)
Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne, shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima. (Ishaya 28:29)
Kakan nuna ƙauna ga dubbai amma kakan hukunta ’ya’ya saboda laifin ubanninsu a bayansu. Ya mai girma da kuma Allah mai iko, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace. (Irmiya 32:18-19)

Sakamakon rashin neman shawarar Ubangiji

Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse. (1 Tarihi 10:13-14)
Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba. Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa. (Yoshuwa 9:14-15)
Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta. (Zabura 106:13-15)
Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. (Zabura 107:10-12)

Ubangiji ne ke iko da shawarar mutane

To, an gaya wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin waɗanda suka hadasa maƙarƙashiya tare da Absalom.” Saboda haka Dawuda ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji ka mai da shawarar Ahitofel ta zama shiririta.” Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya. Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel. (2 Sama’ila 15:31, 33-34)
Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?” To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel. (2 Sama’ila 16:20, 23)
Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.” Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau. Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba. Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’ Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne. “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama. Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai. In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.” Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa. Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka. Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ” Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin. Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta. Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi. Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?” Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima. Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.” Saboda haka Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka tashi suka ƙetare Urdun. Kafin wayewar gari, babu wanda ya rage da bai haye ba. Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya hau jakinsa ya koma gidansa a garinsu. Ya kintsa gidansa sa’an nan ya rataye kansa. Ta haka ya mutu, aka kuma binne shi a kabarin mahaifinsa. (2 Sama’ila 17:6-23)

Nassi

Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. (Zabura 119:24)

Mutane masu ibada

Uwa da uba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado. (Karin Magana 1:8-9)
Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana. (Karin Magana 6:20-22)
Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa. (Karin Magana 23:22)

Misalin shawarar uba mai ibada

Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’ (1 Sarakuna 2:1-4)

Waɗanda aka ba su baiwar hikima

Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. (2 Tarihi 9:23)
Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani. (Karin Magana 13:20)
Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. (1 Korintiyawa 12:8)

Mutane masu ƙwarewa

Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima. (1 Sarakuna 12:6-8)
Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima. (2 Tarihi 10:6-8)

Shawarar da za a guje wa

Mugaye

Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi? Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye. (Ayuba 21:14-16)
Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. (Zabura 1:1)
Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne. (Karin Magana 12:5)

Misalin mugun shawara

Sai mutanen da suke zama a wurin suka fara yin ƙoƙari su sa mutanen Yahuda su karaya, suka sa su ji tsoron ci gaba da ginin. Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa. (Ezra 4:4-5)
Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci yana ba da mugayen shawarwari. (Nahum 1:11)

Masu bautar gumaka

Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu. (Maimaitawar Shari’a 32:28)
Na duba amma ba kowa ba wani a cikinsu da zai ba da shawara, ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su. Duba, dukansu masu ƙarya ne! Ayyukansu ba su da riba; siffofinsu iska ne kawai da ruɗami. (Ishaya 41:28-29)

Tsofaffi

Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima. Ya tambaye su, “Mece ce shawararku? Yaya za mu amsa wa waɗannan mutane masu cewa, ‘Ka sassauta nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?” Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri. Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi. Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.” (1 Sarakuna 12:8-10, 13-14)
Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima. Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?” Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri. Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan, ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.” (2 Tarihi 10:8-10, 13-14)

Albarka da la’ana

Albarka da amfanin neman shawara

Nasara

Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara. (Karin Magana 11:14)
Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara. (Karin Magana 15:22)
...don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa. (Karin Magana 24:6)

Ja-gora da shiriya

Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai. (Zabura 32:8)
Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. (Zabura 73:24)
Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana. (Karin Magana 6:20-22)

Hikima

Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara. (Karin Magana 13:10)
Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima. (Karin Magana 19:20)

Farin ciki wajen ba da shawara

Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki. (Karin Magana 12:20)

La’ana da sakamakon rashin neman shawara ko neman shawarar mugaye

Mutuwa

Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse. (1 Tarihi 10:13, 14)
Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa. Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni; (2 Tarihi 22:3-5)
Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.” (2 Tarihi 25:16)
Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna, da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba, Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku, sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba, da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata, za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su; (Karin Magana 1:24-32)

Faɗa

Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara. (Karin Magana 13:10)

Shirye-shirye sun lalace

Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara. (Karin Magana 15:22)

Kasawa

Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara. (Karin Magana 11:14)

La’anoni da sakamako dabam-dabam

Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba. Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa. (Yoshuwa 9:14-15)
Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta. (Zabura 106:13-15)
Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. (Zabura 107:10-12)