Ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da dukiya
Ra’ayin Ubangiji game da arziki
Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. (Ru’uya ta Yohanna 2:9)
Ra’ayin mutane game da dukiya
...mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa. (Ayuba 5:5)
Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba. (Ayuba 15:29)
Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa. (Ayuba 20:10)
Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su. (Ayuba 20:15)
Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba. Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba. “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba. (Ayuba 20:18-20)
...duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa. (Ayuba 20:26)
Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah. (Ayuba 20:28)
Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama. (Ayuba 21:13)
Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye. (Ayuba 21:16)
In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka. Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu, sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka. (Ayuba 22:23-25)
“Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki. (Ayuba 27:13)
Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa, abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa. (Ayuba 27:16-17)
In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya. (Ayuba 36:11)
Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci? (Ayuba 36:19)
Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana. Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi. (Mai Hadishi 7:11-12)
Ba za mu ɗauki kome tare da mu sa’ad da muka mutu ba
Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru; gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba. Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara, zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba. Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. (Zabura 49:16-20)
Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi, ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa. Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa. (Mai Hadishi 5:13-15)
Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. (1 Timoti 6:7)
“Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba. (Zabura 39:6)
Ba za ka iya sayen fansar ranka ba
Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni, waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu? Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi, kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa, (Zabura 49:5-8)
Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa. (Karin Magana 11:4)
Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? (Mattiyu 16:26)
Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? (Markus 8:36-37)
Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa. (Luka 9:25)
Arziki yana kawo “abokai” da yawa
Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa. (Karin Magana 14:20)
Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi. (Karin Magana 19:4)
Dukiya mai wucewa ce
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa. (Karin Magana 23:4-5)
Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. (Ibraniyawa 11:24-26)
Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. (1 Bitrus 1:7)
Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, (1 Bitrus 1:18)
Dukan dukiya ba kome ba ce idan aka kwatanta da sanin Yesu
Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi (Filibbiyawa 3:7-8)
Arziki ba tabbatacce ba ne
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (1 Timoti 6:17)
Arziki ba shi da amfani ba tare da Ubangiji ba
Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa. Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni. Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so. Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba. Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata. Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya. (Mai Hadishi 2:4-11)
Abubuwan da suka fi arziki daraja
Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba. Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba. Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai. Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba. (Ayuba 28:15-19)
Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa; (Zabura 37:16)
Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa. (Zabura 119:14)
Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. (Zabura 119:72)
Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla, (Zabura 119:127)
Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi, gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita. Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma. (Karin Magana 3:13-16)
Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla, gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita. (Karin Magana 8:10-11)
Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau. Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya, ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika. (Karin Magana 8:18-21)
Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala. (Karin Magana 15:16)
Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya. (Karin Magana 16:8)
Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa! (Karin Magana 16:16)
Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai. (Karin Magana 16:19)
Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne. (Karin Magana 19:1)
Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja. (Karin Magana 20:15)
An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya. (Karin Magana 22:1)
Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne. (Karin Magana 28:6)
Za a bukaci abu mai yawa daga wanda aka ba wa abu mai yawa
Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi. (Luka 12:48)
Albarkar dukiya
Za a sāka wa masu adalci da wadata
Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali. (Karin Magana 13:21)
Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala. (Karin Magana 15:6)
Dukiya ga wanda yake tunani a kan Maganar Allah
Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara. (Zabura 1:1-3)
Masu wadata za su yi wa Ubangiji sujada
Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba. (Zabura 22:29)
Addu’a domin wadata
...don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo. (Zabura 106:5)
Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” (Zabura 122:6-7)
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, (Zabura 128:5)
Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya. (3 Yohanna 2)
Masu ibada mawadata
Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana. (Farawa 12:5)
Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya. (Farawa 13:2)
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa. (Farawa 15:13-14)
Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya. (Farawa 24:1)
Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro. (Farawa 24:16)
Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna. (Farawa 24:35)
Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. (Farawa 26:12-14)
Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna. (Farawa 30:43)
Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa. (Farawa 33:11)
Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. (Farawa 41:42)
Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.” (Farawa 45:13)
Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar. (Farawa 46:6)
To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai. (Farawa 47:27)
...ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da ’yan’uwanku.” (Yoshuwa 22:8)
To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz. (Rut 2:1)
“Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya. (2 Sama’ila 1:24)
Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina. Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba. (1 Sarakuna 10:4, 7)
Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. (1 Sarakuna 3:11-13)
Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. (1 Tarihi 29:23)
Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki. (1 Tarihi 29:28)
Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.” (2 Tarihi 1:11-12)
Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya. (2 Tarihi 9:22)
Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma. (2 Tarihi 17:5)
Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai. Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda (2 Tarihi 17:11-12)
Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure. (2 Tarihi 18:1)
Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki. Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai. Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi. (2 Tarihi 32:27-30)
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma. (Nehemiya 9:25)
...yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa. (Ayuba 1:3)
Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon. (Daniyel 3:30)
Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. (Mattiyu 27:57)
Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku! Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; (1 Korintiyawa 4:8, 11-12)
Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. (Filibbiyawa 4:11-18)
Ubangiji yana jin daɗin wadatar bayinsa
Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.” (Zabura 35:27)
Ba duka ne za su wadata ba
Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka. Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu. (Ibraniyawa 11:36-40)
Yesu ya cancanci ya karɓi arziki
Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” (Ru’uya ta Yohanna 5:12)
Masu hikima za su iya zama mawadata
Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai. (Karin Magana 14:24)
Yadda ake samun dukiya
Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta; ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja. (Karin Magana 24:3-4)
Abubuwan da ke hana mutane samun dukiya
Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba. (Karin Magana 21:17)
Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta. (Karin Magana 22:16)
Haɗarin dukiya
Son dukiya
Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu. (Zabura 62:10)
Girman kai
Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka. Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma. (Ezekiyel 28:4-5)
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (1 Timoti 6:17)
Kada mawadata su yi girman kai domin rai gajere ne
Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa. (Yaƙub 1:9-11)
Ka yi taƙama da Ubangiji ba da arziki ba
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa, amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan, cewa ya fahimci ya kuma san ni, cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri, gaskiya da kuma adalci a duniya, gama a waɗannan ne nake jin daɗi,” in ji Ubangiji. (Irmiya 9:23-24)
Arziki yana ba da jin kwanciyar hankali
Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci. (Karin Magana 10:15)
Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba. (Karin Magana 18:11)
Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.” Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro. (Zabura 30:6-7)
Waɗanda suke dogara ga arziki
Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu. Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. (Zabura 49:10-12)
Dukiya tana raba mutane
Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna. Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba. Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne. Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne. Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.” Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.) Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna. (Farawa 13:5-11)
Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa. Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.” (Farawa 26:12-16)
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub. Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu. (Farawa 36:6-7)
Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar. (Ishaya 5:8)
Arziki zai iya raba Kiristoci
Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan! (1 Korintiyawa 11:18-22)
Arziki mai ruɗi ne / zai iya shaƙe ’ya’ya
Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce. (Karin Magana 11:18)
Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani. (Mattiyu 13:4-5, 7, 22)
Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce, “Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba. Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar, amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani. (Markus 4:2-3, 7, 18-19)
Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su. Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. (Luka 8:7, 14)
Yana da wuya mawadaci ya shiga Mulkin
To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.” Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’” Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?” Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.” Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai. Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama. Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.” (Mattiyu 19:16-26)
Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’” Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.” Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai. Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!” Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah! Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.” (Markus 10:17-27)
Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.” (Luka 18:28-30)
Mawadatan da ba su san Ubangiji ba za a raba su da shi har abada
“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa. “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’ “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. (Luka 16:19-25)
Mawadata suna zaton su masu hikima ne
Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai. (Karin Magana 28:11)
Yadda mawadata suke bi da matalauta
Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya. (Karin Magana 18:23)
Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne. (Karin Magana 22:7)
Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba? (Yaƙub 2:6-7)
Dukiya na iya sa a manta da Ubangiji
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba, gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi, ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba. (Maimaitawar Shari’a 6:10-12)
...ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku. Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba. To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna, sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya. Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.” Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau. (Maimaitawar Shari’a 8:9-18)
Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina. (Maimaitawar Shari’a 31:20)
“Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna. (Karin Magana 30:7-9)
Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba. Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka. (Irmiya 22:21-22)
Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani. (Ru’uya ta Yohanna 3:17-18)
Dukiya tana haifar da hassada
Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. (Farawa 26:12-14)
Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.” (Farawa 26:16)
Yaƙub ya ji cewa ’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.” (Farawa 31:1)
La’anonin dukiya
La’anar sacewa
Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana. (Karin Magana 13:8)
La’anar rashin barci
Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci. (Mai Hadishi 5:12)
Kaitonku ga mawadata
“Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami ta’aziyyarku. (Luka 6:24)
Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. (Yaƙub 5:1-5)
Me ya sa mugaye suke wadata?
Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni. (Zabura 10:3-5)
Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta; gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu. Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu. Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar. A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba. Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama. (Zabura 37:1-2, 7, 9-11)
Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya. Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga. Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?” Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya! Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai. (Zabura 73:1-20)
Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya. (Karin Magana 11:16)
Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa? Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu. (Irmiya 12:1-2)
Mawadata marasa ibada
A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel. (1 Sama’ila 25:2)
Kwanaki 180 cif, ya nuna yawan dukiyar masarautarsa, da ɗaukakarta da kuma darajar girmansa. (Esta 1:4)
...ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan ’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni. (Esta 5:11)
Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka. (Ishaya 2:7)
Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya. (Ezekiyel 27:33)
“Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka. (Daniyel 11:2)
Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. (Luka 19:2)
An umarce mu kada mu nemi wadatar wasu mutane
Kada ku yi yarjejjeniyar abuta da su, muddin kuna da rai. (Maimaitawar Shari’a 23:6)
Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’ (Ezra 9:12)
Hanyar wadata da ba daidai ba
Wasu suna wadata ta wurin zunubi ba tare da yarda da zunubin ba
Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.” (Hosiya 12:8)
Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba. (Zakariya 11:5)
Wasu suna nuna kamar masu addini don su wadata
Mika ya ce, “Yanzu na san cewa Ubangiji zai yi mini alheri, da yake Balawen nan ya zama firist nawa.” (Mahukunta 17:13)
Dabam-dabam
...in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya, (Karin Magana 2:4)
Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce. (Mai Hadishi 10:20)
Wasu lokuta mutane suna yaudara game da yanayin kuɗinsu
Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai. (Karin Magana 13:7)
An yi amfani da kuɗi don kwatanta darajar Mulkin Allah
“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar. “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi. (Mattiyu 13:44-46)
An daidaita rayuwar adalci da azurfa
Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani. (Karin Magana 10:20)
Hukunci a kan al’ummai mawadata marasa ibada
Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su. (Ishaya 15:7)
Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke. (Irmiya 51:13)
Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kin ce, ya Taya, “Ni kyakkyawa ce cikakkiya.” “ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma. “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla. “ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai. “ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya. “ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu. “ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi. “ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar. Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji. “ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai. “ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki. “ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya. “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke. A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau. “ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama masu jigilar kayanki. Kin cika da kaya masu nauyi a tsakiyar teku. Matuƙan jiragenki sun kai ki can cikin manyan tekuna. Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu a tsakiyar teku. Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki, ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki, ’yan kasuwarki da dukan sojojinki, da kuma kowa da yake cikin jirgi zai nutsa a tsakiyar teku a ranar da jirginki zai nutse. (Ezekiyel 27:3, 12-27)
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado. Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu. (Hosiya 10:1-2)
Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace. Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.” Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan. (Zefaniya 1:11, 13, 18)
Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna. Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta. (Zakariya 9:3-4)
Kada sarki ya yi arziki fiye da kima
Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.” Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba. (Maimaitawar Shari’a 17:16-17)
Sarakuna sun ƙi bin umarnin kada su yi arziki fiye da kima
Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu, da kuma dawakai dubu goma sha biyu (1 Sarakuna 4:26)
Nauyin zinariya da Solomon yake samun kowace shekara, talenti 666 ne. Ban da haraji daga ’yan kasuwa, da fatake, da kuma daga dukan sarakunan Arabiya, da gwamnonin ƙasar. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na zinariya. An yi kowace garkuwa da zinariya bekas ɗari shida. Ya kuma yi ƙananan garkuwoyi ɗari uku na zinariya. An yi kowane garkuwa da zinariya minas uku. Ya sa su a cikin Fadar Kurmin Lebanon. Sa’an nan sarki ya yi kujerar sarauta mai nauyin giram na hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki. Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon. Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri. Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya. Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai. Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima. Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai. An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye. (1 Sarakuna 10:14-28)
Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai, ya kasance da kekunan yaƙi dubu da ɗari huɗu da kuma dawakai dubu goma sha biyu, waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, da kuma tare da shi a Urushalima. Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka. Aka shigo da dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye ’yan kasuwan fada suka saye su daga Kuye. Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. (2 Tarihi 1:14-17)
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.” Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba. (Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja. Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.) Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya. Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne, ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya. Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon. Sai sarki ya yi wata kujerar sarauta mai girma da aka shafe ta da hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu sun tsaya a kan matakalai shida, ɗaya a ƙarshen matakala guda. Ba a taɓa yin irin wannan abu don wata masarauta ba. Dukan kwaf na Sarki Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon zinariya ne zalla. Ba a yi wani abu da azurfa ba, domin ba a ɗauki azurfa a zamanin Solomon a bakin kome ba. Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai. Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya. Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai. Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima. Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka. (2 Tarihi 9:8-27)
Annabci
Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki. (Zabura 45:12)
Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba. Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.” Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki. Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji. (Ishaya 39:2, 4-6)
Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji. Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja. Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe, ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba, saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai, sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara. (Ishaya 60:5-6, 9, 11)
Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama. A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu. (Ishaya 61:6-7)
Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Haggai 2:7)
“Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ” (Zakariya 1:17)
Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ” (Zakariya 7:7)
Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! (Ru’uya ta Yohanna 6:15-16)
Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. (Ru’uya ta Yohanna 13:16-17)
Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. (Ru’uya ta Yohanna 17:4)
Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.” (Ru’uya ta Yohanna 18:3)
“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ (Ru’uya ta Yohanna 18:11-19)
An yi amfani da begen dukiya a matsayin ƙarfafawa
Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.” Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma ’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya. Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.” (Farawa 34:10-12)
Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro ’ya’yansu mata, su kuma su auri namu. Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.” (Farawa 34:21, 23)
Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.” (1 Sama’ila 17:25)